Ogbadibo
| Wuri | ||||
|---|---|---|---|---|
| ||||
| Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | |||
| Jihohin Najeriya | Jahar Benue | |||
| Yawan mutane | ||||
| Faɗi | 130,988 (2006) | |||

Ogbadibo daya ce daga cikin kananan hukumomin dakejihar Benue Nijeriya. Ogbadibo ƙaramar hukuma ce ta jihar Benue, arewa ta tsakiya, Najeriya. Tana da gundumomi uku wato: Orokam, Owukpa, da Otukpa. Hedikwatar Karamar Hukumar tana cikin Garin Otukpa.
Tana da faɗin ƙasa da yakai girman 598 km2 da yawan jama'a da suka kai kimanin 128,707 a ƙidayar shekarar 2006.
Manyan yan Najeriya daga Ogbadibo
[gyara sashe | gyara masomin]Tsohon Ministan Noma da Raya Karkara Manomi Marubuci Dan siyasa Audu Ogbeh Audu Ogbeh
Cif Steven Lawani Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Benue Dan siyasa Masana'antar Steven Lawani
Manjo Janar Chris Abutu Garuba Soja Tsohon Gwamnan Jihar Bauchi kuma Babban Jami'in Sa ido na Sojoji na Majalisar Dinkin Duniya Angola II Chris Abutu Garuba
Tsohon Ministan Ilimi kuma marubuci Jerry Agada[1]
Dr Paul Enenche, Babban Fasto na Cibiyar Bishara ta Duniya ta Dunamis.
Lambar gidan waya ta yankin ita ce 973.[2]
Yanayi
[gyara sashe | gyara masomin]Ogbadibo na da yanayi mai zafi irin na damina da rani, inda ruwan sama ya fi yawa tsakanin watan Afrilu zuwa Oktoba, yayin da lokacin rani ke fuskantar tasirin iskar Harmattan. Zafin jiki yakan kasance mai ɗumi a duk shekara, galibi tsakanin 22°C (72°F) da 34°C (93°F), sannan matsakaicin ruwan saman shekara yana tsakanin milimita 1,200 zuwa 1,600 (inci 47–63).[3]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ name=https://punchng.com/ex-minister-agada-dies-in-benue-isolation-centre/
- ↑ "Post Offices- with map of LGA". NIPOST. Archived from the original on 2012-11-26. Retrieved 2009-10-20.
- ↑ "Weather Dallas". meteoblue (in Turanci). 2025-11-28. Retrieved 2025-11-28.
